Kamar yadda kafar yada labarai ta Sky News ta ruwaito, a jiya, Juma’a 11 ga watan Agusta, wasu masallata 8 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon ruftawar wani masallaci a birnin Zariya na jihar Kaduna, dake arewacin Najeriya.
Abdullah Kwarbai kakakin karamar hukumar Zaria ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a lokacin da daruruwan masallata ke gudanar da sallar Juma'a a babban masallacin birnin.
Ya kara da cewa: Da farko an gano gawarwaki hudu, sannan kuma jami'an ceto sun gano wasu gawarwaki bayan kwashe tarkacen masallacin da ya ruguje.
Rushewar gine-gine a Najeriya, kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a Afirka, yana yin sanadiyyar mutuwar mutane da dama.